Arzikin Najeriya Ba Zai Girgiza Ba - inji Kwastom

Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Abdullahi Dikko Inde, tare da wasu manyan jami'an hukumar

A dai dai lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriya ke kokarin kare kanta daga tabarbarewar tattalin arziki, a sanadiyar faduwar farashin mai a kasuwar duniya.

Hukumar Kastam ta Najeriya tace idan aka jajirce wurin inganta aikin karbar haraji a sassa daban daban na Najeriya, arzikin Najeriyar bazai girgizaba.

Shugaban hukumar Kastam Abdullahi Dikko Inde, shine ya bayyanawa manema labaru haka a Abuja alokacin da hukumarsa ke bukin cika shekara ‘daya da kirkiro sabon tsarin nan na karbar haraji a tashoshin jiragen ruwa dana sama a Najeriya.

Bayan da hukumar Najeriya ta ba hukumar Kastam damar karbe aikin nan da ‘yan kwangila keyi na tara haraji domin Najeriya. Shirin da ya kawo cece kuce a lokacin da aka karbeshi daga hannun ‘yan kwangila.

Shugaban hukumar Kastam din Abdullahi Inde, ya bayyana cewar hukumar Kastam din tayi tarihi na tara harajin daya kai Naira Biliyan sau Biliyan wato Tiriliyon daya kenan na Naira a karshen wannan shekarar da ake ciki.

Your browser doesn’t support HTML5

Abdullahi Dikko Inde - 3'13"