Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Rasha Ya Bar Kano


Jirgin Rasha a Kano, Disamba 7, 2014.

Masu sharhi ka al’amurran yau da kullum da sauran ‘yan Najeriya na ci gaba da fadin matsayin su game da jirgin sama na daukar kaya mallakar sojin kasar Rasha da jami’an tsaro suka kama makare da makamai a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.

A halin yanzu dai, mahukuntan Najeriya sun bada izinin tashin wannan jirgi kwana biyu bayan hana jirgin tashi da kuma tsare ma’aikatan da suka tuko shi.

Da missalin karfe tara saura kwata na maraicen jiya ne, jirgin ya tashi daga Filin Jiragen Saman Mallam Aminu Kano, bisa umarnin mahukuntan Najeriya.

Kafin a kai ga wannan mataki sai da gamayyar kungiyoyin matasan arewa suka shafe yinin jiya Litinin a filin jirgin saman, suna zanga-zangar lumana ta neman bayanai daga hukumomin Najeriya, game da wannan jirgi tare ma da rera wakoki na ‘yanci.

Matashi Nura Umar cewa yayi “wannan zalunci ne domin wannan irin zalunci a zo maka da makamai jiharka, ka tsaya kuma kana bincike ba’a sanar da kai ba zai tashi sai dai ya tashi yayi tafiyar sa kasan akwai cikakken zalunci a ciki.”

Masu kula da al’amura dai na cewa akwai darussan koyo game da wannan danbarwa. Mallam Habu Ahmed wani mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum a Kano.

“Darasi shine mutane sun fara gane hagunsu dakuma damarsu, sun fara fuskantar abubuwan da zai cutar dasu, kuma sun fara ganewa cewa mulkin dimokaradiyya ba mulkine daya bada dama ayi danniya ba.”

Wasu daga cikin matasan masu zanga-zangar sun nuna rashin jin dadinsu game da umarnin mahukunta na sakin jirgin da aka kama dauke da manyan makamai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG