Auren Jaruma Halima Atete Da Angonta Mohammad

Halima Atete da Mohammad (Hoto: Instagram/Adbulamart mai kwashewa)

Za a daura auren na a ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Jarumar Kannywood Halima Atete za ta amarce tare da angonta Mohammed Mohammed Kala.

Za a daura auren ne a ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Furodusa Abdulamart Mai Kwashewa ne ya wallafa hotunan masoyan biyu hade da katin gayyata.

“Allah ya tabbatar da Alheri Sarauniya @haleemaatete.” Abdulamart ya ce.

Jarumi Ali Nuhu ma ya wallafa hoton Atete hade da katin auren, a wani mataki na taya masoyan biyu murna.

Gabanin daurin auren, akwai shagulgula da wasanni da za a gudanar kamar wasan kwallo, Margi Day da dai sauransu kamar yadda katin gayyatan ya nuna.