Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Yi Shagulgulan Bikin Mawaki Abdul D. One


Abdul D One da amaryarsa Salma (Hoto: Instagram/Ali Nuhu)
Abdul D One da amaryarsa Salma (Hoto: Instagram/Ali Nuhu)

“Allah ya sanya alkairi ango,” fitaccen mawaki Umar M. Shareef ya wallafa a shafin Instagram din mawakin.

A karshen makon da ya gabata ne fitaccen mawakin Kannywood Abdulkadir Tajuddeen, wanda aka fi sani da Abdul D One ya angwance da amaryarsa Salma.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa an daura auren masoyan ne a ranar Lahadin da ta gabata a unguwar Tudun Murtala da ke birnin Kanon Najeriya.

Jaruman Kannywood maza da mata sun hallara a wajen shagulgulan bikin, ciki har da jarumi Ali Nuhu da iyalansa.

Ali Nuhu (farko daga dama) tare da iyalinsa da ango Abdul D One da amarya Salma (Hoto: Instagram/Ali Nuhu)
Ali Nuhu (farko daga dama) tare da iyalinsa da ango Abdul D One da amarya Salma (Hoto: Instagram/Ali Nuhu)

Tun a makon jiya da aka fara yada hotunan shirye-shiryen auren ma’auratan, inda abokanan huldar mawakin da masoyansa suka yi ta addu’o’in taya murna.

“Masha Allah, Allah ya sanya alheri,” In ji Jaruma Rukayya Dawayya.

“Allah ya sanya alkairi ango,” fitaccen mawaki Umar M. Shareef ya wallafa a shafin Instagram din mawakin.

Shi ma fitaccen furodusa Bashir Maishadda ya taya mawakin murnar wannan aure inda y ace, “Allah ya sanya alkhairi. Ameen summa ameen.”

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG