Ba a Samu Bullar Polio ko Sau Daya a Jihar Kaduna a 2013 Ba

Bayar da maganin rigakafin Polio a Kaduna

Jihar Kaduna ta doshi kawar da cutar Polio baki daya a bayan da aka shafe shekarar 2013 ba tare da bullar wannan cutar ba
A bayan da aka samu bullar cutar Polio har sau 15 a Jihar Kaduna a shekarar 2012, an shafe shekarar da ta shige ta 2013 ba tare da samun ko da yaro guda daya da ya kamu da wannan cuta a cikin jihar ba.

Jami'in yada labarai na hukumar kula da lafiya tun daga tushe a Kaduna, Hamza Ibrahim Ikara, ya fada a wata tattaunawa da Muryar Amurka cewa wannan nasara ta samu ne a saboda namijin yunkurin da gwamnatin jihar ta yi, da kuma irin hadin kan da aka samu daga al'ummar jihar, manya da kanana.

Yace a shekarar ta 2013 an gudanar da kyamfe har sau 9 na bayar da rigakafin a fadin jihar, sannan an gudanar da wani aikin na musamman guda, wadanda duk suka taimaka wajen cimma wannan tazara.

Jami'in yada labaran yace ba wai kawai maganin rigakafin cutar Polio suke bayarwa ba, su na bayar da na dukkan cututtukan da suke addabar yara, yana mai rokon iyaye da su tabbatar sun kare lafiyar 'ya'yansu ta hanyar samar musu da rigakafin.

Your browser doesn’t support HTML5

An Samu Gagarumar Nasara Wajen Yaki da Polio a Jihar Kaduna a 2013 - 2:58