Accessibility links

Jami'in Rotary Ya Yaba Ma 'Yan Jarida Masu Yaki Da Polio


Aikin rigakafin Polio na Kungiyar Rotary a Kaduna, Najeriya (Rotary International)

Jami'in na kungiyar Rotary a Jihar Katsina, Muhammad Amin, yace kungiyar ta fii kowane bangare tasiri wajen fadakar da jama'a amfanin yin rigakafin Polio

Wani jami;i na kungiyar Rotary International a Jihar Kastina, arewa maso yammacin Najeriya, yace kungiyar 'Yan jarida Masu Yaki da Cutar Polio, JAP a takaice, ita ce zata fi taka rawa wajen wayar da kan jama'a game da muhimmancin yin rigakafin cutar Polio.

A lokacin da yake magana awurin wani taron da Muryar Amurka ta shirya a Katsina, malam Muhammad Amin na kungiyar ta Rotary, yace irin wannan muhimmancin shi yasa ya nemi sanin matsayin wannan kungiya a jihar Katsina da isarsa can, a bayan da ya yi aiki a jihohi irinsu Borno, Yobe, Bauchi da kuma Kano.

Malam Muhammad Amin yace su ma hukumomin lafiya na duniya dake dafawa kokarin na yaki da cutar Polio, kamar Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, sun gano irin muhimmancin da kungiyar take da shi, har sun bullo da wani sabon shiri na tallafawa 'ya'yan kungiyar da kudade domin gudanar da ayyukansu na wayar da kai.

Yace ita ma kungiyarsu ta Rotary International, daya daga cikin manyan masu tallafawa kokarin kawar da cutar Polio daga doron duniya, zata zauna da kungiyar 'yan jaridar domin nazarin hanyar da zata iya taimaka mata wajen gudanar da ayyukan fadakarwa.

XS
SM
MD
LG