Ba Ma Goyon Bayan 'Yan Biafra - Okorocha

Gwamnan Imo Rochas Okorocha

Gwamnan jihar Imo kuma shugaban gwamnonin jam'iyyar APC yace kungiyar nan mai suna MASOB dake fafutikar neman kafa kasar Biafra bata da goyon bayan kabilar Igbo.

Mr Rochas Okorocha gwamnan jihar Imo ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa kungiyar nan mai rajin kafa kasar Biafra bata da goyon bayan kabilar Igbo.

Gwamna Okorocha ya yi wannan furucin ne a garin Bauchi a arewa maso gabashin Najeriya kana ya kara da cewa gwamnonin APC suna bada goyon bayansu akan yaki da 'yan Boko Haram.

Gwamnan yace sun bada goyon bayansu ga gwamnatin tarayya ta taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa dasu. Kuma ashirye suke su ba shugaban kasa kowane irin taimako ya nema wurinsu.

Halin shugaban kasa Buhari su ne ya sa aka soma samun canji tun daga lokacin da ya hau mulki, inji Gwamnan Okorocha. Yace ba shawo kan Boko Haram kadai ba har ma an samu canji a samun wutar lantarki saboda shugaban kasa mutum ne mai gaskiya. Mutane na daukan maganarsa da mahimmanci.

Gwamna Okorocha ya alakanta kungiyar MASOB da iskanci saboda babu wani shugabanta na takamaimai. Tuk wanda aka tuntuba zai ce shi bashi da hannu ciki.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ba Ma Goyon Bayan 'Yan Biafra - Okorocha