Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Cafke Wata 'Yar Kunar Bakin Wake a Adamawa


Sojojin Najeriya

Sojoji dake jihar Adamawa a kauyen Kubula sun cafke wata dake kokarin kai harin kunar bakin wake.

Sojojin sun cafketa ne yayinda take kokarin kaucewa sojoji domin kaiga inda zata tarwatsa bam din dake cikin jakarda take boye da ita.

Bayan binciken kwakwaf sojojin sun sake gano wasu abubuwa masu fashewa kusa da inda suka cafke yarinyar. Sojojin sun kuma samu sun kashe wasu su hudu dake kokarin tada bamabamai.

Kwamandan sojojin yace sun ji labarin shirin da suke yi sai suka yi masu kwantan bauna suka gama dasu kafin su isa inda su mutane hudun suka yi niyar tada bamabaman.

Kwamandan yace da ikon Allah sai sun kakkabe duk 'yan ta'ada kamar yadda shugaban kasa ya bada umurnin su yi.

Su ma 'yan sakai da 'yan kato da gora suna bada taimako wurin yaki da 'yan Boko Haram saboda ganin an kawo karshen aika-aikarsu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG