Bayer Leverkusen Ta Kori KWach Nata Sami Hyypia Yau Asabar - 5/4/2014

Kungiyar kwallon kafar Bayer Leverkusen ta Jamus ta sallami kwach din ta Sami Hyypia a yau asabar din nan, a bayan da ta fuskanci kalubale sosai a wasanninta na baya-bayan nan, kuma a yanzu ma tana fuskantar barazanar zamewa daga matsayi na 4, abinda zai hana ta samun shiga gasar cin kofin zakarun kulob na Turai a shekara mai zuwa.

An nada kwach na kungiyar matasan kulob din, Sascha Lewandowski, ya rike Leverkusen har zuwa karshen kakar kwallo ta bana.

Leverkusen ta sallami kwach din nan take, a bayan da jiya jumma’a ta sha kashi a hannun Hamburg SV wadda take can kasa a teburin Bundesliga, inda a yanzu Wolfsburg da Borussia Moenchengladbach su na iya shige ture ta daga matsayi na 4 a wasannin da zasu yi yau asabar.

A farko farkon wannan kakar kwallo, Leverkusen ita ce ta biyu a teburin Bundesliga, amma a wasanni 12 na bayan nan da ta yi, kwaya 3 kawai ta samu nasarar lashewa. Haka kuma ta sha kashi sosai a hannun PSG ta Faransa a gasar cin kofin zakarun kulob na Turai da kuma Kaiserslautern a gasar cin kofin kalubalenka na Jamus.

Your browser doesn’t support HTML5

Bayer Leverkusen Ta Kori Kwach Nata - 1'00"