BELGIUM: An Soke Bukin Sabuwar Shekara Bisa Dalilan Tsaro

A Belgium, magajin Brussels, babban birnin kasar, ya soke bikin shekara-shekara na shigar sabuwar shekara na bana, saboda an sami rahotanni kanbarazanar ta'addanci.

Magajin garin, Yvan Mayeur, wanda yayi magana da kafofin yada labaran kasar, yace, cibiyar da take nazarin bala'o'i, tace da wuya a tantance dubun dubatan mutane da zasu hallara a dandalin bukukuwan shiga sabuwar shekarar.

A farkon makon nan 'Yansandan kasar, suka kama mutane biyu kan zargin suna shirya makarkashiyar harin ta'addanci, kan abunda jami'an tsaron suka kira cibiyoyi na tarihi ko masu muhimanci. Masu gabatar da kara a gaban kotu, sun kira barazanar a zaman "mai tsanani."

Hudu daga cikin maharan da suka kai farmaki a birnin Paris cikin watan Nuwamba, 'yan kasar Belgium ne.

Ahalinda ake ciki kuma, dubban 'Yansanda ne wasu dauke dogayen bindigogi, da na'urorin gano makamai masu guba da ire-irensu, da karnuka masu iya gano abubuwa, suna daga cikin gungun jami'an tsaro da zasu samar da tsaro a dandalin Times dake birnin New York, a bukin shigar sabuwar shekara, da za'a yi can anjuma da dare.