Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Faransa Suna Neman Mutum Na Biyu Kan Hare-haren Paris


Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande

Jami'an Faransa suna neman mutum na biyu da aka kyautata zato yana da alaka da hare-haren da aka kai Paris

Jami'an kasar Faransa suna neman mutum na biyu da ya gudu wanda yake da alaka da hare-haren da aka kai kan Pris babban birnin kasar.

Jami'an uku da suka yi magana jiya Talata da sharadin baz a'a ambaci sunayensu ba saboda basu da izinin yi magana sun ce bincike ya nuna mutumin yana da hannu dumu-dumu cikin kai hare-haren na ranar Juma'a 13 ga wannan watan.

A wani halin kuma hukumomin Faransa da na Belgium sun bada umurnin a kama wani mutum mai suna Salah Abdelsalam. Jami.an sun yana daya daga cikin maharan.

Mutum na biyu da ya arce har yanzu ba'a san inda yake ba.

XS
SM
MD
LG