Dan Shekara 13 Ya Bada Duk Abin Daya Mallaka Ga Wata Maras Lafiya

Jesse Kaufman tare da Jasmine Boden

Wani yaro dan shekara 13 da haihuwa, yayi abinda akasarin samari masu shekarunsa ba zasu iya yi ba, watau ya dauki kudade masu yawa da aka tara masa na Ajo a lokacin bukin zamowarsa saurayi, ya je ya bayar gudumawa ga wata ‘yar makarantarsu wadda ya karanta labarin cewa tana fama da cutar sankarar kwakwalwa.

Shi dai wannan yaro sunansa Jesse Kaufman, kuma yana karanta jaridar garinsu shekarun baya, sai ya ga labarin wata yarinya ‘yar shekara 9 mai fama da cutar sankarar kwakwalwa. A lokacin shi ma yana dan shekara 9, sai ya fasa asusunsa, yaga yana da kudi dala 20 a lokacin, watau kimanin naira dubu 4, sai ya sa mahaifiyarsa ta aika ma iyayen wannan yarinya a zaman gudumawarsa.

Wani ikon Allah, shekara guda bayan wannan, sai suka kasance cikin aji daya a makarantar Midil ta Gateway, suka zamo abokan juna.

A cikin watan Agustar da ya shige, Jesse ya cika shekaru 13 da haihuwa, kuma a bisa al’adarsu, akan tara jama’a a yi wa yaro kayan ajo, domin daga wannan lokacin ana daukar cewa ya zamo magidanci, shi ba yaro ba ne. An tara ma Jesse kudi har dala 4,800. Sai yaje ya roki iyayensa da su cika masa dala 200 domin kudin ya zamo dala dubu biyar daidai, suka cika masa, suka ce mai zai yi da shi, shi ne yace yana so ne ya bayar gudumawa ga wannan ‘yar ajinsu, Jasmine Boden, mai fama da cutar sankarar kwakwalwa.

Dala dubu 5 din nan, kimanin Naira miliyan daya ne. Haka Jesse ya tattara wannan kudin kai ma abokiyarsa Jasmine domin ta kara a kan kudin jinyar da take yi, har zuwa wani asibiti a Jihar Massachussetts daga jiharsu ta Pennsylvania.

Jasmine ta fadawa gidan rediyon KDKA a garinsu cewa tana godiya maras iyaka da irin wannan tallafi da dan ajinsu Jesse ya bayar da ma illahirin mutanen wannan garin.

Duk da haka dai, wannan yaro dan shekara 13 bai tsaya a nan ba, domin ya kafa wani asusun neman taimako ta kan yanar gizo ko intanet, inda yace yana kokarin tara wani dubu 5 din domin taimakawa Jasmine.

Hausawa suka ce, na Allah ba zai taba karewa ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Dan Shekara Sha Uku da Kyautar Girma - 2'04"