Dokar Karin Yawan 'Yan Majalisu

Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar.

Yan majalisun dokokin Nijer sun jefa kuri’ar na’am da wata sabuwar dokar da ke kara yawan yan majalisun dokikin kasar daga 113 zuwa 171 a wata majalisar da ake sa ran zaben manbobinta ta shekara mai zuwa ta 2016.

Gwamnatin kasar dai tace tayi karin adadin yan majalisar ne sakamakon yawan jama’ar kasar da ya karu zuwa million 17 da yan kai, inda doka tace kowane mutum dubu ‘dari zai samu wakilcin mutum daya a majalisa,

To amma sai dai yan adawa sunki jefa kuri’ar tare da cewar lokaci bai yiba takamata yayi ace majalisar bata kara yawan membobi ba.

Saurari cikakken rahoton Abdoulaye Mamane Amadou daga Niamey.

Your browser doesn’t support HTML5

Dokar Karin Yawan 'Yan Majalisu a Nijer - 4'47"