Accessibility links

Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa ta Karyata Cewa ta Baiwa Shugaba Jonathan Gudumawar Naira Milyan Biyu

  • Aliyu Imam

Gungun 'yan Najeriya.

Da yake magana kakakin kungiyar komared Bashir Madara yace wanda akace yayi magana a madadin kungiyar basu ma san da zamansa ba.

Gamayyar kungiyoyin matasan Arewa sun nesanta kansu da rahotan dake cewa wai a ranar asabar din data gabata sun bada gudunmawa naira miliyan biyu ga takarar shugaba Goodluck Jonathan, yayin da a hannu guda kuma sukayi Allah wadai da gudunmawar kimanin naira miliyan goma da akace daluban jihar Kano sun baiwa gwamna Rabiu Musa Kwankwaso domin ya sayi form din neman shugabancin najeriya.

Kakakin gamayyar kungiyoyin komorade Bashir Madara, yace basu san da wannan kungiya ko mutumin da yayi magana a amdadinsu ba, saboda baya cikin 'yan gwagwarmaya.

Da yake magana kan haka, wani malamin jami'a Dr. Sa'id Ahmed Dukawa, yace yin haka idan ya tabbata da gaskene, ya sabawa dokar zaben kasa.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG