Accessibility links

Al'ummomin da Rikici Ya Tarwatsa a Jihar Nasarawa Na son Komawa Gidajensu


Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nassarawa

Cikin 'yan watannin nan jihar Nasarawa ta shiga jerin jihohi dake fama da rikicin kabilanci wanda yayi sanadiyar tarwatsa al'ummomi da dama da arcewa daga muhallansansu.

Yanzu al'ummomin sun koka da irin halin kuncin da suke ciki.

Shugabannin al'ummomin suna kokarin sasanta kansu domin zaman lafiya ya dawo kana su samu su koma gidajensu a yankunan da suka fito.

Ardon Fulani Ciroma Lawal yace rugage suna cikin gari maimakon cikin daji kuma babu wurin zama. Yace hankalinsu a bace yake domin damina ta karato. Shi ma sarkin noman Asakyo Anglo Ode yace abun da ya faru ya jefa manoma cikin wahala. Babu yadda zasu yi. Ga abinci a gona ga yara sun bazu ko ta ina basu san yadda zasu yi ba. Su manoma suna kuka da rokon Allah ya tabbatar masu da zaman lafiya.

Onarebu Ismaila Ishaleku daga karamar hukumar Obi yace suna cikin wani mummunan hali ne wanda bashi da dadi. Mutum na ganin gidansa amma ba zai iya shiga ba har da ma sarakunansu duk basa gidajensu.

Duk yawancin 'yan gudun hijiran suna cikin garin Lafiya ne inda gwamnatin jihar ta taimaka masu da kayan abinci da kayan kwana da magunguna har da ma kudade domin rage masu radadin rayuwa.

Halidu Garba Sako sakataren sarkin Agya yace idan an hada kabilun wuri daya aka tattauna za'a samu masalaha. A nasu wurin sun dauki matakai tare da kiran sarakuna da shugabannin Fulani su kira yaransu dake rike da makamai su hada kai kowa ya koma inda yake zaune da can domin a samu zaman lafiya.

Shugabannin suna ganin nan da 'yan kwanaki kadan kowa zai koma gurbinsa domin ganin irin taimakon da gwamnan jihar yayi. Ban da kayan abinci, na wanki da na kwana gwamna ya baiwa al'ummomin kowace karamar hukuma da lamarin ya shafa nera miliyan daya.

Gwamnan ya basu tabbaci cewa kafin a soma bada katin zabe na din-din-din wata mai zuwa zasu koma gidajensu.

Sakatariyar gwamnatin jihar Hajiya Zainab Abdulmummuni tace abu mafi mahimmanci shi ne kowace kabila ta nemi hanyar zaman lafiya. Mutanen kowane wuri su karfafa zaman lafiya tsakaninsu da junansu. Tace duk inda aka samu matsala gwamna na zuwa kana a aika masu kayan tallafi. Hatta sansanin 'yan gudun hijira yana zuwa kuma ya kai tallafi.

Za'a soma raba katin zabe ranar tara ga wata mai zuwa. Katin ba a zabe ya saya ba. Kati ne na shaida da mutum zai rike. Ya zama wajibi a koma kan zaman lafiya domin a soma aikin cikin kwanciyar hankali.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG