DOMIN IYALI: Bibiya Kan Dokar Takaita Kayayyakin Aure A Gumel, Kashi Na Biyar, Yuli, 29, 2021

Alheri Grace Abdu

Idan kuna biye da mu shirin Domin Iyali ya karbi bakuncin masu ruwa da tsaki a Karamar Hukumar Gumel ta jihar Jigawa domin fahimtar dokar da ta haramta yin kayayyakin aure da suke wuce kima, da nufin fahimtar yadda zata amfani iyali. Bakin yau ma muna tare da Hon Salisu Abdullahi Gumel, sakataren cibiyar yaki da aikata miyagun laifuka a Karamar Hukumar, da kwamred Yahaya Shu’aibu Ngogo dan gwaggwarmaya mai fafatukar kare hakkin iyali, da kuma Barrista Amina Umar Hussein sakatariyar kungiyar mata ta kasa da kasa FIDA reshen jihar Kano.

Saurari ci gaban bayanin Hon Salisu kan hujjar kafa dokar a tattaunawar da wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta:

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI:Bibiya Kan Dokar Takaita Kayayyakin Aure A Gumel Kashi Na Biyar-10:00"