Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Bibiya Kan Dokar Takaita Kayayyakin Aure A Gumel, Kashi Na Daya, Yuni, 24, 2021


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Idan kuna biye da mu makon da ya gabata shirin Domin Iyali ya fara haska fitila kan dokar da aka kafa a Karamar Hukumar Gumel ta jihar Jigawa dake haramta yin kayayyakin aure da suke wuce kima. A yau mun gayyaci masu ruwa da tsaki domin nazarin yadda wannan dokar zata amfani al'umma ba tare da tauye hakin wani bangare ba.

Bakin da shirin ya gayyata su ne, Hon Salisu Abdullahi Gumel, sakataren cibiyar yaki da aikata miyagun laifuka a Karamar Hukumar Gumel da Kwamred Yahaya Shu’aibu Ngogo dan gwaggwarmaya mai fafatukar kare hakkin iyali, da kuma Barrista Amina Umar Hussein sakatariyar kungiyar mata ta kasa da kasa FIDA reshen jihar Kano.

Saurari tattaunawar da Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta:

DOMIN IYALI:Bibiya Kan Dokar Takaita Kayayyakin Aure A Gumel Kashi Na Daya-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:58 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG