DOMIN IYALI: Zargin Magidanci Da Bata 'Ya'yansa Kanana-Kashi Na Uku.

Grace Alheri Abdu

Yau ma zamu dora a bibiya da shirin Domin Iyali ya ke yi kan lamarin da ya faru a Layin Mallam Bello dake garin Kaduna inda wata mace ke neman taimakon al'umma da masu hali baiwa musamman kungiyar lauyoyi mata da kungiyoyin kare hakkin kananan yara domin neman hakinta da na.

Masu saurare dake biye da wannan shirin da dama sun aiko da sakonni ta waya da kuma email suna nuna bayyana niyarsu ta marawa wannan yunkuri na ganin wadannan kananan yara sun zauna a yanayin da zasu samu walwala da rayuwa mai inganci, burin da mahaifiyarsu take nanata a hirarta da Domin Iyali.

Shirin ya samu zantawa da Hajiya Sa’adiya Isa Suleiman, shugabar kungiyar Babajo Disabled and Orghanage Foundation, wadda ta bayyana matakan da suka dauka na taimakawa Fatima dangane da wannan lamarin.

Saurari cikakken shirin

Your browser doesn’t support HTML5

Zargin Magidanci Da Bata 'Ya'yansa Kanana-Kashi Na Uku-!0"