Donald Trump Ya Zabi Nikki Haley A Matsayin Jakadiyar Amurka A MDD

Nikki Haley

Yau Laraba shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, ya ayyana gwamnar Jahar North Carolina, Nikki Haley a matsayin Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya. Kuma itace mace ta farko da ya nada a majalisar zartaswarsa.

‘Yar shekaru 44, Haley, wacce asalin iyayenta ‘yan kasar Indiniya ne, ta na kan wa’adinta na biyu ne a matsayin gwamnar Jahar ta North Carolina, sai dai ba ta kwarewa kan harkokin difilomasiyya.Ita ce kuma ta farko ta zama da Mr. Trump ya zaba a gwamnatinsa, wacce ba farar fata ba.

A lokacinda yake ayyanata, Trump ya ambato ziyarar aiki data kai kasashen waje da nufin kulla yarjejeniyar cinakkaya a madadin jahar Carolina ta arewa, da kuma shawarwari da kamfanoni na kasashen ketare.

Gwamna Haley dai bata goyi bayan Trump ba, lokacinda ake yakin neman zaben fidda dan takara.