Farfasa Osinbajo Ya Gamsu da Aikin Gyaran Filin Jirgin Sama Na Abuja

Farfasa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasar Najeriya

Jim kadan bayan ya duba aikin da aka yi wajen gyara filin jirgin sama na kasa da kasa dake Abuja, Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Farfsa Yemi Osinbajo, ya nuna gamsuwarsa bisa ga aikin da aka yi.

Inji Farfasa Osinbajo yace ya zagaya filin da kansa, ya duba aikin ya kuma saurari bayanai daga jami'an dake sa ido akan aikin da 'yan kwangilar da suka yi aikin da jami'an ma'aikatar sufurin jiragen saman Najeriya, ya gano an yi gagarumin aiki sosai.

Yace 'yan kwangilar sun yi hobasa irin wanda suke tsammani saboda sun yi aiki ba dare ba rana kuma zasu kammala komi da komi kafin jibi Laraba, ranar da za'a sake bude filin domin jirage su soma jigilar fasinjoji kamar da.

Shugaban hukumar jiragen saman Najeriya Injiniya Saleh Dunoma yace ko a yanzu jirage na iya sauka a filin. Shi ma Injiniya Muhammad Kiyari Sandabi wani mai yawan tafiye tafiye ta jirgin sama yace babu shakka an cimma abubuwan da ake bukata kuma suna alfahari da abubuwan da aka yi.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Farfasa Osinbajo Ya Gamsu da Aikin Gyaran Filin Jirgin Sama Na Abuja - 2' 08"