Garkuwa Da Mutane Na Shafar Lafiyar Kwakwalwarsu - Masana

Tashar Jirgin Kasa A Kaduna

Masana kundin tsarin mulki sun ce ya kamata gwamanti ta yi duk mai yiyuwa wajen kubutar da metanen da ke hannun yan bindiga.

A daidai lokacinda ake kan neman bakin zare ga matsalolin tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa a Najeriya musamman ma arewacin kasar, masana kundin tsarin mulki sunce saboda muhimmancin ran dan adam ya kamata gwamanti ta yi duk mai yiyuwa wajen kubutar da metanen da ke hannun yan bindiga, bisa la’akari da ilollin da sace mutane ke da shi ga lafiyar kwakwalwa kamar yadda masana halayyar dan adam suka bayyana.

‘Yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wadanda ke tsare a hannun ‘yan bindiga a daji, da wadanda ‘yan bindiga suka kaiwa farmaki a kauyukansu suna neman gwamnati ta kawo musu dauki doń kubutar da ‘yan uwan nasu.

Sace-sacen mutane don karbar kudin fansa ko a bisa wata manufa na daban abu ne da ya zamo ruwan dare musamman a arewacin Najeriya, kuma a baya-bayan nan matsalar na kara ta’azarra, lamarın da ya fara kai ga ‘yan bindigar sace kananan yara ‘yan kasa da shekara daya zuwa bakwai a duniya dama mata.

Ko menene ilollin sace mutane musamman kananan yara ga lafiyar kwakwalwarsu, masaniya a fannin ilimin yara, Hauwa Mustapha Babura, ‘yar asalin jihar Jigawa kuma mazauniyar kasar Amurka na da bayanin cewa yana taba kwakwalwar da ake kira ta uku a yara da ka iya haifar masu da damuwa da sa su rashin iya koyar abubuwa.

Ku Duba Wannan Ma Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayyar Najeriya Ta Kaddamar Da Samame Akan Sansanonin ‘Yan Bindiga 

A bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya me ya kamata gwamnati ta yi wajen ceto wadanda ke tsare a hannun ‘yan bindiga da suka bayyana cewa ba zasu yi magana da iyalan wadanda suka sace ba sai da gwamnati.

A hirar shi da Muryar Amurka, barista Mainasara Kogo fitaccen lauya a Najeriya ya ce tsaron jama’a da na dukiya shine mafi karancin hakkin da ya ke a wuyan hukuma.

Ya zuwa yanzu dai fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna dake tsare a daji sun kwashe akalla kwanaki 30 ba tare da sanin makomarsu ba.

A baya dai gwamnatin kasar ta ce tana aiki tukuru wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa a kasar, duk da cewa wasu ‘yan kasar na ganin har yanzu bata cansa zani ba.

Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulrauf:

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Ilolli Mara Misaltuwa Ga Lafiyar Kwakwalwar Yara Da Manya Da ‘Yan Bindiga Ke Sacewa - Masana