Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Ce Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 70 A Wani Samame Da Suka Kai Ta Sama


Jirgin yakin Najeriya mai daukar sojoji da manyan makamai
Jirgin yakin Najeriya mai daukar sojoji da manyan makamai

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kashe mayakan ISWAP fiye da 70 a arewacin kasar da ke kan iyaka da Nijar, a wani samame da ta kai ta sama.

Sanarwar ta ranar Asabar ta ce haddin gwiwar jiragen sama daga Najeriya da Nijar ne ya kai samamen.

Yankin tafkin Chadi, inda Najeriya ta ce ta kaddamar da farmakin ta sama, ya shahara wajen karbar bakuncin mayakan kungiyar IS da ke yammacin Afirka (ISWAP), kungiyar masu dauke da makamai tun shekarar 2016.

Tare da tsofaffin abokan hamayyar Boko Haram, bangarorin biyu sun kashe sama da mutane 40,000 a cikin shekaru goma da suka gabata. Sama da mutane miliyan biyu ne har yanzu ke gudun hijira daga gidajensu saboda tashe-tashen hankula da ake ci gaba da yi.

Kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet, ya ce, “Ayyukan da aka gudanar a ranar 13 ga Afrilu, 2022, sun gano wasu ‘yan ta’adda da dama, da yiwuwar wani sansani.

Sanarwar ta kara da cewa, a sakamakon haka, sun kai hare-hare ta sama a ranar 14 ga watan Afrilu a Tumbun Rego da kuma wani sansanin horaswa da ke kusa.

"Sama da 'yan ta'addar ISWAP 70 aka kashe ko kuma suka ji munanan raunuka," in ji shi.

Najeriya kan yawaita kai hare-hare a wannan lokaci kafin a fara shiga damina.

Sojoji sun shafe fiye da shekaru 12 suna fafatawa da mayakan. Hakazalika, sojojin gwamnati na fafatawa da wasu gungun 'yan bindiga masu dauke da muggan makamai a yankin arewa maso yamma da kuma rikicin 'yan aware a yankin kudu maso gabas.

Tun a shekarar da ta gabata, ISWAP ta fi samun karbuwa daga hannun Boko Haram bayan da shugabanta Abubakar Shekau ya mutu a rikicin da ya barke tsakanin su.

Shekau dai ya shahara a duniya ne bayan sace ‘yan mata kusan 300 a garin Chibok a shekarar 2014.

~ Al-Jazeera

XS
SM
MD
LG