Gawar Kofi Anan Ta Isa Kasar Ghana

Kofi Anan

Yau Talata shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo tare da wasu tawaga ta mussamam , ya karbi gawar marigayi Kofi Anan in da aka saukar da tutocin Majalisar Dinkin Duniya da ta Ghana kasa kasa, alamar cewa an mikawa Ghana gawar.

Gawar ta isa filin saukar jirgin sama na Kutuka International Airport, inda yan jarida na gida da na ketare suka halarci taron yayin da dangi da abokan arziki suka taru a filin cikin koke koke da jimamin rashin yayin da ake sauke gawar ta Kofi Anan.

Daular Asantima wanda ita ce shine asalin Kofi Anan ta gabatar da addu’a da jawabi kan rayuwar marigayin kamar yadda al’adar su ta tanada.

An shimfida gawar Kofi Anan a babban dakin taron Accra International Conference Center ta yadda al’ummar kasar za su samu damar gabatar da girmamawar su ta karshe tare da yin bankwana da shi.

Ranar Laraba babban sarkin Asantawa zai gabatar da al’addunsu kansancewar sun lakabawa marigayin sarautar Busumuru na Asantawa. Daga bisani kuma ranar Alhamis za’a shimfide gawar Kofi Anan a babban dakin taron Conference Center na Accra inda manya kawai da shuwagabanni da mambobin Majalisar Dinkin Duniya za su gabatar da girmamawar su. Za’a binne gawar Kofi Anan a sabon makabartar sojoji ta kasar bayan kammala bukuwan al’adun su.

Your browser doesn’t support HTML5

Gawar Kofi Anan Ya Issa Kasar Ghana 2'56