GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Agusta 23, 2018: Rayuwar Kunci Da 'Yan Najeriya Ke Shiga A Saudiya

Grace Alheri Abdu

Yau shirin Domin Iyali ya yada zango kasar Saudiya, sai dai ba batun aikin hajji zamu nazarta ba. Wannan karon zamu tabo wata matsala da aka dade ana Ambato sai dai kawo yanzu, babu takamammen matakin da aka iya dauka na shawo kan matsalar, Watau batun jan ra’ayin mutane musamman mata da ‘yammata su tafi kasar Saudiya da nufin neman ingancin rayuwa, sai dai idan suka isa wurin su tarar ba haka lamarin yake ba. Wakilin Sashen Hausa Lamido Abubakar yayi kicibis da wannan lamarin yayin aikin hajji da yaje. Ya kuma yi hira da wadanda suke ganau na wannan lamarin, da kuma matakan da hukumomin Najeriya suka fara dauka na shawo kan matsalar.

Saurari cikakken shirin

Your browser doesn’t support HTML5

Halin kunci da 'yan Najeriya ke shiga a Saudiya-10"