Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Agusta 16, 2018: Matsalar Shan Miyagun Kwayoyi A Arewacin Najeriya


Grace Alheri Abdu

Matan gwamnonin arewacin Najeriya sun fara dauka mataki na shawo kan matsalar shan miyagun kwayoyi da ta ta'azzara a yankin, dake barazana ga ci gaba da kuma dorewar iyali

Kamar yadda muka alkawarta maku, yau shirin Domin Iyali zai yi bibiya kan matakan da matan gwamnonin arewacin Najeriya suka fara dauka na dakile matsalar shan miyagun kwayoyi dake barazana ga ci gaban iyali. Bayan kaddamar da shirin a jihar Sokoto, wakilin Sashen Hausa Murtala Faruk Sanyinna ya tattauna da uwargidan gwamnan jihar Hajiya Mariya Waziri wadda ta bayyana matakan da suke dauka a kungiyance na shawo kan wannan matsalar.

Saurari Cikakken shirin.

Matsalar shan miyagun kwayoyi a Najeriya-10:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:26 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG