Gwamnan Jihar Ekiti Ya Kaddamar Da Yakin Sake Neman Zabensa

Babban taron APC a Lagos

Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, yace zai kara himmar ci gaba da samar da kayayyakin more rayuwa ma al’ummar jihar idan suka sake zabensa a matsayin gwamnansu.

Gwamna Fayemi yana magana ne a filin wasa na Oluyemi Kayode dake Ado-Ekiti, babban birnin jihar, a lokacin da yake kaddamar da yakin sake neman zabensa.

Gwamna Fayemi yayi ikirarin cewa ya samar da ayyukan yi tare da inganta hanyoyin kiwon lafiya a jihar, abubuwan da yace zai ci gaba da yinsu idan aka sake zabensa.

Filin was an ya cika makil da ‘ya’yan jam’iyyar APC na ciki da wajen jihar, wadanda suka zo kaddamar da yakin neman zaben gwamnan.

Za a gudanar da zaben gwamnan na Eikiti a watan Yuni.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal daga garin Ado Ekiti

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Eikiti Dan APC Ya Kaddamar Da Yakin Neman Zabensa - 1'33"