Accessibility links

An Kira 'Yan Arewa dake Kudancin Najeriya da Su Hada Kai da Jami'an Tsaro


Mai Martaba Sarkin Musulmi Alhaji Mohammed Sa'ad Abubakar III
Tashin tashinar da 'yan Boko Haram ke yi a arewa da kuma barazanar kai hare -hare da tayi kan jihohin kudancin kasar ya sa duk wasu 'yan arewa dake zuwa cirani a jihohin kudu sukan fada hannun mahukunta dake daukansu 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Sanadiyar irin mawuyacin halin da 'yan arewa ke fuskanta a kudancin kasar musamman a jihohin kudu maso yamma ya sa 'yan arewa mazauna jihohin suka kafa wata kungiya ta hada kawunan 'yan arewa da cigabansu. Kungiyar ta yi kira ga ilahirin 'yan arewacin Najeriya dake kudu maso yammacin kasar da su hada kai da jami'an tsaro.

Kungiyar ta umurci mutane su dinga nemo takardar shaida daga inda suka fito da inda zasu domin kaucewa fadawa hannun jami'an tsaro kamar yadda ya sha faruwa cikin 'yan kwanakin nan. Shugaban kungiyar na kasa Alhaji Hassan Isyaka Tafidan Ibadan ya yi wannan kiran a karshen taronsu na wata wata da suka yi a Ibadan cibiyar gwamnatin Oyo. Yace suna kira ga 'yan arewa dake zuwa jihohin Oyo, Osun , Ondo, Ogun, Ekiti da Legas domin neman aikin leburanci ko yin sana'a idan zasu taho su nemi mai anguwa ko dagaci ko shugaban karamar hukuma su tabbatar sun karbo wata 'yar sheida da zata nuna inda suka fito. Su kuma tantance inda zasu da sunan wanda zasu wurinsa. Yin hakan zai basu sauki kuma zai hana yin awongaba da ake yi da 'yan arewa da basu da wata kwakwarar sheida.

Da basu da kungiya da take yiwa 'yan arewa magana ta karesu idan jami'an tsaro sun cafkesu kan rashin yadda dasu. Kungiyar mai harshe daya an kafata ne ta taimaki 'yan arewa 'yan cirani domin kada su fada cikin wani wahalar da basu san hawa ba balantana sauka. Kungiyar zata kare mazauna jihohin da dukiyoyinsu da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Shugaban yace sun samu goyon baya daga wurin iyaye da suka yi na'am da kungiyar. Hatta Sarkin Musulmi ya goyi bayan kungiyar ya kuma yi masu addu'a. Duk sarakunan hausawa dake jihohin kudu maso yamma su ne iyayen kungiyar. Kungiyar bata da alaka da siyasa amma tana alaka da duk 'yan siyasa. Kowane dan siyasa na iya shiga kungiyar amma bata siyasa ba ce.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.
XS
SM
MD
LG