Gwamnati Na Daukar Matakan Sulhu Tsakaninta Da 'Yan Shi'a - Dambazau

ABUJA: 'Yan Shi'a sun yi zanga zanga

Ministan kula da harkokin cikin gida a Najeriya, Janar Abdurrahman Dambazau mai ritaya, ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya na daukar duk wani matakin da ya kamata na sulhu tsakaninta da kungiyar 'yan shi'an domin kaucewa rikici.

"Akwai abubuwan da ake yi na bayan fage wanda za a samu a tattauna da mutane domin a duba abin yi. Saboda haka duk matakan da ya kamata a dauka gwamnati tana yi domin tabbatar da bukatarta na samar da zaman lafiya a kasa." inji Dambazau

To amma wannan sulhun zai yi tasiri idan har gwamnati ba ta sako shugaban mabiya shi'an, Ibrahim El-Zakzaky kamar yadda kotu ta bada umarni yi?

Dambazau ya amsa da cewa:

"Gwamnati na daukar matakan da za su kawo zaman lafiya tunda duk wanda ya ce shi dan Najeriya ne, ai ba zai so tashin hankali ba, zai so ne a zauna lafiya.

To sai dai masu sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriya na ganin lallai gwamnati ta jawo wannan kungiyar a jiki ba wai ta rika amfani da matakin karfi akan su ba.

"Ya kamata gwamnati ta yi kokarin ganawa da shugabanninsu don mutane ne masu girmama shugabanninsu kuma suna jin maganarsu. A nuna musu su ma mutane ne, a sauraresu idan har aka yi haka za a samu maslaha," inji Ibrahim Katsina, mai tsokaci kan harkokin tsaro.

Saurari cikakken rohoton Umar Farouk Musa

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnati Na Daukar Matakin Sulhu Da 'Yan Shi'a - Dambazau - 4' 03"