Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Sun Sake Kama ‘Yan Shi’a 20 a Abuja


Kungiyar ‘yan Shi’a mabiya Ibrahim El-Zakzaky a Najeriya ta bijirewa jami’an tsaro, inda ta sake tura mutanenta suka ci gaba da yin zanga-zanga da caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kungiyar ta zargi ‘yan sanda da hana kai abinci ga wadanda aka tsare a ofishin jami’ai masu yaki da ‘yan fashi da ake kira SAS su 150, wadanda suka ce sai bayan da aka matsa lamba aka fara basu abincin.

Masu zanga-zangar dai sun dage sai an sako shugabansu Ibrahim El-zakzaky da ke tsare biyo bayan arangamar almajiransa da sojoji a birnin Zariya cikin shekarar 2015.

‘Yan kungiyar dai sun bayyana a Abuja ta bangaren kasuwar Wuse, da ci gaba da muzaharar. Jami’in labaran kungiyar na Abuja Saminu Azare, ya ce an sake kama mutane 20 kuma an kai wanda yaji rauni a ka asibiti.

A cewar mai sharshi kan al’amuran yau da kullum Yusuf Isihak Baje, faifan bidiyon da aka watsa dake nuna abin da wasu daga cikin masu zanga-zangar suka yi na daukar makamai suna jifan jami’an tsaro, dole ne ‘yan sanda su dauki matakin kare kansu.

Sai dai jami’in labaran kungiyar Saminu Azare ya nuna jajircewarsu da cewa ba zasu yi ‘kasa a gwaba ba wajen fitowa da nunawa duniya irin zaluncin da ake musu.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG