Gwamnatin Jihar Neja Ta Bada Tabbacin Sake Tsugunar Da Mutanen Da Tashin Hankalin ‘Yan Bindiga Ya Raba Da Muhallansu 

Gwamnatin Jihar Nejan Ta Bada Tabbacin Sake Tsugunar Da Mutanen Da Tashin Hankalin ‘Yan Bindiga Ya Raba Da Muhallansu

Bayanai dai sun tabbatar da cewa akwai daruruwan mutanen da suka bar garuruwansu saboda tashin hankalin ‘yan fashin daji masu satar mutane domin neman kudin fansa da wani lokaci ma suke halaka jama’a.

NIGER, NIGERIA - A lokacin da yake jawabi a bikin bada sanda ga sabon Sarkin Kagara, Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya ce zasu ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyon baya domin tabbatar da samun cikakken tsaro a Jihar.

A nashi gefen sabon Sarkin na Kagara, da ta sha fama da wannan tashin hankali na ‘yan bindiga, Alhaji Ahmed Garba Attahiru II, ya ce matsalar rashin tsaron ta durkusar da tattalin arzikin yankin saboda haka suna bukatar gwamnati ta sake duban yankin.

Shi ma dai shugaban karamar hukumar Rafi, Alhaji Isma’ila Modibbo ya yi karin haske akan bakar wahalar da suka sha a hannun maharan.

A yanzu dai gwamnati ta sha alwashin maida hanakali ga muggan mutanen nan da ake kira Infoma masu bayyana wa ‘yan bindiga bayanan sirri.

Saurari cikakken rahoton daga Mustapha Nasiru Batsari:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Nejan Ta Bada Tabbacin Sake Tsugunar Da Mutanen Da Tashin Hankalin ‘Yanbindiga Ya Raba Da Muhallansu .mp3