Har Yanzu Wasu Daliban Buni Yadi na Cikin Daji

Gawarwakin dalibai a kwalejin gwamnatin taraiya inda aka kashe dalibai 59, Fabrairu 25, 2014.

Yayinda hukumomi a jihar Yobe, arewa maso gabas a Najeriya ke cewa suna cigaba da daukar matakai, domin gani komai ya dai-daita a makarantun kwana a jihar, Iyaye da harin ranar Talata da harin ya rutsa da ‘ya’yansu a makarantar gwamnati na Yadi Buni, har yanzu suna cikin tashin hankali, biyo bayan rashin ganin ‘ya’yansu.
Wasu daga cikin iyayen da basa so a fadi sunayensu, sun tattauna da Muryar Amurka inda wani uba yake cewa “mu iyayen yara mun shiga halin innalilLahi wa inna ilaihirraji’un. Muna neman taimako a wajen gwamnati, yaran mu sun shiga cikin daji.”

Wata mahaifiya tace “tun ranar da abun ya faru, walLahi har yau hankalinmu ba a kwance yake ba. Har yanzu bamu ga wasu yaranmu ba”.

Wata yarinya dake makarantar a lokacin da maharan suka isa ta bada labarin abunda ya faru a lokacin da ‘yan bindigan suka shiga makarantar. Tace “sun ce mana, kar mu sake dawowa makarantar, idan muka dawo zasu hallaka mu baki daya.

Har yanzu bayanai na nuna cewa akwai sauran yaran makarantar da suka gudu a daji.

Your browser doesn’t support HTML5

Daliban Makarantar Buni Yadi na Cikin Daji - 3'30"