Hotunan Labaran Duniya na Ranar Talata 20 Ga Watan Yuni Shekarar 2017

Wani mai wa'azi ya durkusa yana addu'a tare da yin kuka a mujami'ar Pentecostal dake sansanin 'yan gudun Bidi Bidi na arewacin Uganda

 

Wani mutune yana ratsawa ta cikin ruwa a kasar India
 

Wani matashi a cikin wani kwale-kwale yana kwasar sharar da za a iya sarrafa ta a birnin Jakarta na Indonesia

 

Uwargida Kate ta Cambridge (Hagu) tana murmushi yayin da take tafiya tare da Yarima William da Yarima Edward a lokacin gasar tseren dawakai a Ascot Ingila

 

Yara suna karawa a gasar koyon kariya a Xi'an Shaanxi dake China Ju.


 

An gudanar da Bikin Dragon Canoe Festival,da kabilar Miao ta yankin Taijiand dake jihar Guizhou ke yi a kasar China.


 

Furen na bullowa a garin Frankfurt, dake kasar Jamus.

 

Wasu mutane na shan hantsi a gabar tekun Saint-Malo a yammacin Faransa
 

Wani yaro dan Sudan yana wucewa a kan jaki ta gefen dakarun wanzar da zaman lafiya na UNAMID yayin da suke cikin motarsu mai sulke a garin Golo dake tsakiyar Dafur