Hukumar Leken Asirin Amurka Ta Bayyana Damuwa Kan Wata Fallasa

CIA Hukumar leken asirin Amurka.

Babbar hukumar leken asiri ta Amurka CIA, ta fito fili tana bayyana damuwarta kan fallasar da dandalin tsegumi WiKiLeaks yayi, hukumar tana gargadin cewa "tilas Amurkawa duka su damu kan makomar wannan mataki.

Jiya Laraba, kakakin hukumar yaki yayi magana kan sahihancin kasidu 8,771 da dandalin ya fallasa, amma ya daga cewa babu kokonto kan niyyar dandalin, "na nakasa karfin hukumar wajen kare Amurka daga 'yan ta'adda da wasu makiyanta."


Ya ci gaba da cewa "irin wannan fallasarar ba kadai zai tsaya wajen jefa ma'aikatan Amurka da aikace aikacensu cikin hadari ba, har zai baiwa mahasadan Amurka da bayanai da zai zasu iya yi mana Illa,"kamar yadda kakakin hukumar Jonathan Liu ya fada cikin wani bayani da ya bayar.


Haka nan shima kakakin fadar White House Sean Spicer, ya bayyana damuwa jiya Laraba, ya gayawa manema labarai cewa Amurka "zata farauto masu fallasa sirrin gwamnati."