Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Majalissar Dinkin Duniya Na Taro Akan Korea ta Arewa


Wani wuri da ake gwajin makamai
Wani wuri da ake gwajin makamai

Kwamitin tsaro na MDD yana wani zama a asirce a yau Laraba game da harba makamai masu lizzami da Korea ta Arewa ta gudanar na baya bayan nan.

Wannan lamarin ya tilastawa China yin kira ga Korea ta arewa, da Korea ta Kudu, da kuma Amurka da su dau matakin dakile kaurewar rikici.

Gabanin wannan taron na yau Laraba, ministan harkokin wajen China Wang Yi ya bukaci Korea ta arewa da ta dakatar da gwaje-gwajen makaman, wanda hakan zai iya sa Amurka da Korea ta Kudu su dakatar da atisayen sojin da suke yi na hadin gwiwa.
Mr. Wang ya kwatanta wadannan aikace-aikacen dukkanin banagrorin a matsayin wata kafa ta tada tarzoma yayinda dukkanin bangarorin ke kin janyewa.

Kwamitin sulhun ya kuma yi Allah wadai da kakkausar murya da gwajin makaman na Korea ta Arewa a ranar Talata, kuma yayi mata kashedin cewar hakan na iya haifar da gasar makamai a yankin.

Ministan harkokin wajen Chinan ya yi kashedi ga Amurka da Korea ta Arewa cewar, wannan abun zai haifar da arangama kuma yace akwai ruruwar tsahin hankali a yankin Korea.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG