Hukumomin Nijar za su Mika Wa Gwamnatin Najeriya 'Yan Boko Haram 500

Rahotanni daga janhuriyar Nijar sun bayyana cewa hukumomin kasar na kokarin mika wasu ‘yan boko haram ga hukumomin Najeriya bayan da aka shafe lokaci mai tsawo ana tsare da su a gidajen yari daban daban.

Daruruwan ‘yan boko haram ne aka bayyana cewa hukumomin Nijer ke shirin mikawa hukumomin kasarsu ta asali wato Najeriya, a wani matakin rage cinkoson firsinoni a gidajen yarin Nijer.

Tun farkon bazuwar rikicin boko haram daga Najeriya zuwa yankin Diffa dake kudu maso gabashin Nijar, jami’an tsaron kasar sun yi nasarar cafke ‘yan boko haram da dama wadanda aka ajiye a gidajen kason garuruwan Yamai da Kollo da Kutukale.

Ganin halin da gidajen yarin da aka ajiye ‘yan boko haram suka shiga na yanayin cinkoson ya sa kasashen biyu yanke shawarar tasa keyar wadanda aka tabbatar da kasancewarsu ‘yan asalin Najeriya domin cigaba da zaman wakafi kafin su fuskanci shari’a.

Da ma dai Najeriya da Nijar na da huldar mikawa junansu firsinoni a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, a cewar Bukary Abdulnaser, jami’i a sashen kula da kare hakkokin bil’adama dake ma’aikatar shari’ar Nijer.

Wata majiya mai tushe ta tabbattar da cewa tuni kasashen biyu suka tattauna da juna ta hanyar musayar wasiku game da shirin mika daruruwan mayakan daga hannun hukumomin Nijer zuwa na Najeriya.

Tun barkewar rikicin boko haram a arewa maso gabashin Najeriya, yankin Diffa na kasar Nijer ke dandana kudar sakamakon yawaitar hare haren da su ka yi sanadiyar mutuwar daruruwan bayin Allah, Cikinsu har da dakarun tsaro, da kuma tilastawa jama’a da dama kauracewa matsugunnasu a kewayen tafkin Chadi, lamarin da ya sa gwamnatin ta Nijer kafa dokar ta baci a yankin na Diffa.

Ga Souley Mummuni Burma da karin Bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Nijar zasu mika 'yan boko haram 500 ga na Najeriya - 2'31"