Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Sojojin Nigeria Zasu Iya Cimma Wa'adin Watan Disamba?


Sojojin birged din da ta kwato garin Bama daga hannun 'yan Boko Haram.
Sojojin birged din da ta kwato garin Bama daga hannun 'yan Boko Haram.

A farkon wannan shekara shugaba Muhammdu Buhari na Nigeria,ya baiwa rundunar sojan Nigeria wa'adin watan Disamba na murkushe yan kungiyar Boko Haram.

A farkon wannan shekara, shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya baiwa rundunar sojan kasar wa'adin watan Disamba na murkushe yan kungiyar Boko Haram, da suka yi shekaru shidda suna razana mutane.

Shin kwaliya zata biya kudin sabulu kuwa? Wani mai magana da yawun rundunar sojan Nigeria yace sojoji sun samu nasarar fatattakar yan yakin sa kan daga yankunan da suka mamaye a arewa maso gabashin Nigeria, harma sun kassara iyawar su ta kai munanan hare hare.

To amma wasu mazauna birnin Mauduguri jihar Borno sunce su kam Alhamdulillahi, yanzu basu jin tsoro kamar da. Amma kuma wasu sojoji da suka zanta da Muryar Amirka sunce har yanzu basu da isassun kayayyakin aiki, yan Boko Haram sun fi su makamai, yayinda wani jami'in gwamnatin jihar Borno yace har yanzu akwai wasu wuraren da ake fuskantar barazana

A halin da ake ciki kuma, har yanzu ba'a tura rundunar sojan hadin gwiwa tsakani kasashe makwaptan Nigeria kamar yadda akayi alkawari ba. A saboda haka ne ake tababa ko kuma tambayar cewa, shin yankin da gaske yake yi wajen yaki ko kuma kokarin murkushe yan Boko Haram?

Duk da nasarorin da rundunonin soja suka samu akan yan Boko Haram a bana, David Zoummenou wani baban jami'i a wata cibiyar bincike da nazari dake Afrika ta kudu yace da sauran rina a kaba wajen murkushe yan Boko Haram

Da Alama kuma shugaba Buhari na Nigeria ya fahimci hakan, shi yasa ne ya bada sanarwa a kwanan nan cewa kila a karawa rundunar sojan Nigeria wa'adin ganin bayan yan yakin sa kan.

XS
SM
MD
LG