Ivory Coast: Yau aka fara shari'ar tsohon shugaban kasar a kotun ICC

Lauret Gbagbo tsohon shugaban kasar Ivory Coast

Yau alhamis ne za’a yi ma tsohon shugaban kasa Ivory Coast Lauren Gbagbo shari’a a kotun manyan laifuka ta kasa da kasa dangane da zargin sa da ake yi da sa hannu a yakin basasar da aka yi bayan zaben shekarar 2010 a kasar.

Gbagbo ne tsohon shugaban kasa na farko da za’a tuhuma a kotun dake birnin Hague, kuma za’a tuhume shine akan aikata laifukan cin zarafin bil’adama da ya hada da fyade, da hallaka jama’a a lokacin rikicin da aka kwashe watanni hudu ana yi, wanda yayi sanadiyyar hallaka mutane 3000.

Rikicin ya kare ne a yayin da Faransa, kasar da ta yima Ivory Cost din mulkin mallaka ta tura dakarunta su maido da zaman lafiya su kuma kama Gbagbo wanda ya buya a gidan gwamnatin kasar a lokacin rikicin.

A jiya laraba ne mai gabatar da karar Fatou Bensouda ya bayyana wa manema labarai cewa Manufar shari’ar itace domin a bankado gaskiya ta hanyar shari’a.

Shima tsohon shugaban matasan kasar Charles Ble Goude zai fuskanci shari’a tare da Gbagbo.

Ambada sammaci domin a kamo uwargidan tsohon shugaban domin yi mata shari’a akan laifukan cin zarafin bil’adama.

A shekarar da gabata ne wata kotun kasar ta yanke mata hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kaso.