Jakuna Na Matukar Raguwa a Duniya

Hukumar kula da rayuwar dabbobi ta Majalisar Dinkin Duniya da masu kare hakkin dabbobi na Afirka, sun nuna damuwa ga yadda Jakuna ke matukar raguwa a duniya, saboda kashe su da a ke yi don samun nama da kuma amfani da fatar su wajen magani a kasar China.

Biyo bayan gabatar da wani kuduri gaban Majalisar Dokokin Najeriya wanda yanzu haka ba a kammala mayar da shi doka ba, gwamnatin Najeriya ta haramta kashewa ko cin naman Jaki.

A wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ta yanar gizo, alkaluman taron suna cewa akwai kimanin Jakuna miliyan 40 a fadin duniya.

Lamarin ya ta'azzara ne bayan da 'yan kasar China suka zuba hannun jari a fataucin Jakuna a Najeriya, don amfani da fatar Jakin. Abin da ya haddasa tashin gwauron zabi na Jakuna.

Dan Majalisar Wakilan Najeriya mai sha’awar lamuran kare dabbobi daga cutarwa, Garba Datti Muhammad, ya ce nan da shekara 10 matukar ba a dauki matakan da su ka dace ba, Jakuna za su kare a duniya.

Garba Datti wanda ya gabatar da babban jawabi a taron hukumar kula da dabbobi ta Majalisar Dinkin Duniya da ta Afirka, ya ce wasu kan yanka Jakuna don amfani da fatar ko cin namansa maimakon amfani da Jakunan ga lamuran sufuri a karkara.

Dan majalisar ya ce a yanzu a duk duniya kimanin Jakuna miliyan 40 a ke da su, kuma a na ci gaba da hallaka su da cutar da su ba tare da kula da lafiyar su ko gudunmawar da su ke bayarwa ga tattalin arziki ba.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Jakuna Na Matukar Raguwa a Duniya 3'30"


Your browser doesn’t support HTML5

Jakuna Na Matukar Raguwa a Duniya 3'30"