Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Karamar Hukumar Guzamala Sun Kaura Zuwa Sansanin 'Yan Gudun Hijira


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Kakakin majalisar dokokin jihar Borno Hon. Abdulkareem Lawan ya ce a yanzu haka babu wani jami'in soja ko guda a karamar hukumar Guzamala dake arewacin Borno samakon hare- haren ‘yan ta’addan Boko Haram.

Lamarin ya yi sanadiyar arcewar mutanen dake karamar hukumar zuwa sansanonin 'yan gudun hijira dake wasu garuruwan da ayyuakn ‘yan ta’adda ke da sauki amma kuma yanzu suke cikin wani mawuyacin halin rayuwa.

An fara kai hari a karamar hukumar ne a shekarar 2014, inda aka kashe mutane da dama da jami’an tsaro kana aka kone dukkan gine ginen gwamnati dake garin, wanda hakan yasa mutanen gari kauracewa gidajen su baki daya.

Kakakin majalisar ya ce bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari a kan karagar mulki a shekarar 2015, babban hafsin sojan kasa a Najeriya, Lt. Gen. Tukur Yusuf Buratai ya jagoranci wata runduna inda suka kwato garin na Guzamala daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram.

Kakakin majalisar, Abdulkareem Lawan, ya ce bayan watanni biyu zuwa uku kugiyar ta Boko Haram ta sake kai hari a karamar hukumar wanda hakan yasa mutane sake ficewa daga garin zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira har zuwa lokacin da aka sake yin wani zabe a shekarar 2019.

Ya kara da cewa “muna da garuruwa fiye da 185 a yankin, amma yanzu haka babu mutum koda guda a wurin. A dan haka ina kira ga gwamnatin tarayya ta kawo mana dauki ta maido da zaman lafiya a karamar hukumar Guzamala”.

Wasu mutanen karamar hukumar dake a sansanonin ‘yan dugun hijira da suka tattauna da Muryar Amurka sun bayyana irin wahala da suke sha dasu da ‘ya’yan su.

Saurari rahoton Haruna Dauda Biu cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG