Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakon MDD Ga Najeriya a Ranar Kare Ilimi Ta Duniya


Wasu dalibai a Afirka

Ranar 9 ga watan Satumban kowace shekara na zama ranar da majalisar dinkin duniya ta ware domin bikin bada kariya ga ilimi, da makarantu, da dalibai daga bala’o’i dabam daban da suka hada da ta’addanci.

A sakon ta ga Najeriya majalisar dinkin duniya ta bukaci kasar ta karfafa kariya ga makarantu, da dalibai da malamai.

Sakon na bikin ranar da ke zama na farko a tarihin majalisar ta dinkin duniya, ya ce kawo yanzu akwai bayanai da suka nuna cewar makarantu 910 aka lalata a yankin arewa maso gabashin Najeriya, tare da rufe wasu 1500, sai kuma yara miliyan 4.2 ake fargaban zasu kasa zuwa makarantu a Najeriya.

A cikin hirarshi da Muryar Amurka, Dr. Bashir Yankuzo, malami a jami’ar kimiya da fasaha da ke Minna kuma kwararre ta fuskar ilimi, ya ce "batun bada kariya ga makarantu yana da muhimmancin gaske, kuma wajibi ne akan kowa, yace makaranta wuri ne na ilimi ba wurin yake-yake ba."

Rahoton na majalisar dinkin duniya ya yi bayanin cewar daga shekara ta 2018 zuwa 2019 akwai yara mata 45 daga cikin 57 da aka yi amfani da su wajen kunar bakin wake a yakin kungiyar 'yan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya, bayan 'yan mata 'yan makaranta daruruwa da aka sace a makarantu dabam daban, ciki harda na Chibok, da Dabci da suka ja hankalin kasashen duniya.

Bikin na bana kuma na farko dai yazo ne a dai dai lokacin da aka rufe makarantu sakamakon barkewar cutar coronavirus a duniya, don haka wakilin majalisar ta dinkin duniya a Najeriya mai kula da bada agajin jinkai Mr Edward Kllon, ya bukaci hukumomi su tashi tsaye wajen samar da ingantaccen tsari na bada kariya da kuma inganta ilimi a matakai dabam daban na kasar.

Haka kuma majalisar ta yi suka ga matakan da wasu gwamnatoci ke dauka na maida makarantu kasuwanni ko kuma sansanonin soji da jami’an tsaro da kuma sansanonin 'yan gudun hijira a yankunan da ake fama da rikici.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG