Jami'yun Hamayyar Nijar Sun Nemi ECOWAS Ta Shiga Batun Zabe Mai Zuwa

Jami'yun Hamayya

Jam’iyun hamayya a jamhuriyar Nijar sun aika wa kungiyar ECOWAS wasika domin ta tsoma baki a rikicin da ya ki karewa, tsakanin bangarorin siyasar kasar, game da tsare tsaren zabukan da ake saran gudanarwa a shekarar 2020 da 2021.

Wanzar da dimokaradiya a kasashen Afirka ta yamma na daga cikin mahimman kudirorin da kungiyar CEDEAO ko ECOWAS ta zo da su a baya, sakamakon lura da cewa rashin gudanar da tsarkakekken zabe wani al’amari ne da ya haddasa rigingimu a kasashe masu yawa a yankin, dalili kenan da ‘yan adawa a jamhuriyar Nijar suka ja hankulan kungiyar ta zuba ido akan shirye shiryen zabubbukan masu zuwa, inji shugaban gamayyar jam’iyun Front Patriotique Ibrahim Yacouba.

Wasikar ta ‘yan adawa ta isa ofishin ECOWAS na Abuja ne a lokacin da aka yi katari shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ne ke da shugabancin wannan kungiya.

Shugabar mata a jam’iyar MPN KISHIN KASA Madame Sabo Hajiya Baraka ta jaddada cewa zasu ci gaba da gwagwarmayar ganin an shirya zaben dimkoradiya Nijar.

Ga Cikakken Rahoto Daga Wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Jami'yun Hamayyan Nijar Sun Kira ECOWAS Tasa Hannu A Rikicin Zabe