Janar Alkali: Hukumomi Sun Sha Alwashin Hukunta Masu Laifi

Wasu jami'an 'yansanda

A wani yunkuri na kwantar da hankalin jama'a da rundunar 'yan sandan jihar Filato ta sha alwashin yin aikinta babu sani ba sabo dangane da bacewar Janar Idris Alkali.

Hukumar ‘yan sandan jahar Filato, ta ba da tabbacin amfani da doka wajen gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a jihar dangane da bacewar wani Janar Idris Alkali.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Mathias Tyopev, ya bayyana haka ne yayin da ya ke ba da tabbacin wadanda aka kama ake zarginsu da hannu wajen bacewar tsohon daraktan gudanarwa a shelkwatar rundunar sojoji da ke Abuja, Janar Alkali mai ritaya.

A cewar jami’in ‘yan sandan, wadanda aka kaman aka kuma mika wa ‘yan sandan daga rundunar sojoji ta uku da ke Rukuba a Jos, a yanzu haka su na hannun ‘yan sanda, su na kuma gudanar da bincike don gurfanar da su a gaban kuliya.

A halin da ake ciki dai har yanzu jami’an sojojin na mamaye da yankin Dura Du inda suke neman Janar Idris Alkali, yayin da mafi yawan mutanen yankin suka kaurace wa gidajensu saboda tsoron abin da ka iya faruwa da su, duk da cewa hukumomin tsaron sun ba da tabbacin ba za su ci mutuncin kowa ba face masu laifi.