Jarumin Nollywood Charles Granville Ya Rasu

Charles Granville (Facebook/Daily Trend)

Baya ga shirin “Tinsel” sauran fitattun fina-finan da Charles ya fito, sun hada da “Last Flight To Abuja,” da “Impossible Relationships,” da “Dowry Man.”

Dan wasan kwaikwayon masana’antar Nollywood da ke kudancin Najeriya, Charles Granville ya mutu a cewar jaridar Daily Tribune.

Wata sanarwa da iyalansa suka fitar a karshen makon da ya gabata, ta ce jarumin, wanda ya yi fice sanadiyyar shirin “Tinsel” mai dogon zango, ya rasu ne a ranar Alhamis 21 ga watan Satumba bayan fama da rashin lafiya.

Sanarwar wacce dan uwan mamacin Iyenemri Somiari Granville tya fitar, ta ce za a sanar da ranar da za a yi janai’zar jarumin wanda har ila yau darekta ne kuma furodusa.

Jaridar yanar gizo ta Legit ta ruwaito cewa a ranar 22 ga watan Satumba jarumin ya mutu, amma sai a ranar 23 aka samu labara.

Baya ga shirin “Tinsel” sauran fitattun fina-finai da Charles ya fito, sun hada da “Last Flight To Abuja,” da “Impossible Relationships,” da “Dowry Man.”

Sannan zai fito a wani sabon fim da ake shirin sakewa mai suna “Locked.”