Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fitacciyar Mai Shirya Fina-finai A Najeriya Peace Anyiam-Osigwe Ta Rasu


Marigayiya Peace Anyiam
Marigayiya Peace Anyiam

Peace ta rasu ne bayan da ta kwashe wani tsawon lokaci tana kwance cikin yanayi na suma.

Shugabar kamfanin AMAA da ke shirya bikin karrama jarumai a Afirka, Peace Anyiam-Osigwe Ta rasu.

Wata sanarwa da ahlinta ya fitar ya nuna cewa Peace ta rasu da safiyar ranar Talata.

“Muna sanar da ku mutuwar ‘yarmu, ‘yar uwa, gwaggo, Peace Maria Ogechi Anyiam-Osigwe.” Sanarwar ta ce.

Peace ta rasu ne bayan da ta kwashe wani tsawon lokaci tana kwance cikin yanayi na suma.

'Yar asalin jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, Peace ta taka muhimmiyar rawa wajen dabbaka masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood da sauran nahiyar Afirka.

Ita ta kirkiri kamfanin Africa Movie Academy Awards (AMAA) da ke shirya bikin karrama jarumai a Afirka.

Irin gudunmowar da ta bayar a fannin nishadi a Najeriya ya sa ake yi mata lakabi da “Queen of Nollywood” – wato “Sarauniyar masana’antar Nollywood.”

Ta kuma kasance ita ce shugabar kungiyar masu shirya fina-finai ta (AMP.)

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG