Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kannywood Na Jimamin Rasuwar Ahmad Tage


Ahmad Tage (Instagram/ Ahmad Tage)
Ahmad Tage (Instagram/ Ahmad Tage)

“Mutumin arziki wallahi, mai kirki, ban taba ganin fushinka ba. Ba ka taba fada da kowa ba. Ga ban dariya. Allah ya maka rahama.” In ji Mansura Isah.

Masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya ta shiga yanayi na alhini bayan rasuwar fitaccen jarumi Ahmad Tage, wanda ke yawan fitowa a fina-finan barkwanci.

Tage ya rasu ne a asibitin Muhammad Wase da ke Kano a ranar Litinin bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya, kamar yadda Mujallar Fim ta ruwaito.

Marigayin ya kasance kwararren mai daukan hoton bidiyo (cameraman) gabanin ya shiga harkar fitowa a fina-finan.

Tuni abokanan sana’arsa suka yi ta bayyana alhininsu bisa wannan rashi wanda ga dukkan alamu ya girgiza masana’antar.

“Allah ya yi wa daya daga cikin masu daukar hoto kuma jarumi a masana’antar Kannywood, Ahmad Tage rasuwa. Allah ya jikansa da rahama.” In ji jarumi Ali Nuhu.

Shi kuwa jarumi Sadiq Sani Sadiq bakin sarari ya wallafa a shafinsa na Instagram don nuna alhininsa.

“Allah ya maka rahama Tage, mu kuma Allah ya kyautata karshenmu.” Sadiq ya ce.

“Mutumin arziki wallahi, mai kirki, ban taba ganin fushinka ba. Ba ka taba fada da kowa ba. Ga ban dariya. Allah yamaka rahama.” In ji Mansura Isah.

Mujallar Fim ta ruwaito Shugaban jaruman Kannywood Alhassan Kwalle yana cewa an sallaci mamacin a a gidansa da ke unguwar Sheka Karshen Kwalta da misalign karfe hudu.

Rasuwar Tage na zuwa ne kasa da mako biyu bayan rasuwar fitaccen mawaki Isyaku Forest.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG