Babban ‘dan takarar adawa na APC, Janal Muhammadu Buhari, yayi jawabin karshe kafin gobe Asabar, inda yake cewa baya neman wannan shugabancin don ya sami kudi ko karfin mulki, sai dai don mutane dake ganin zai iya tabuka wajen yakar cin hanci, talauci da inganta tsaro.
Janal Buhari dai ya sake shiga yarjejeniya da shugaba Jonathan, kan tabbatar da lumanar bayan zabe yace magoya bayansa kan iya kula da kuri’unsu bisa tanadin doka.
‘Dan takarar adawar dai ya nuna rashin sanin yakamata ne yadda yaji labarin wasu mutane na sayar da katin zaben su, ya kuma ce wannan alamar mutuwar zuciya ce da rashin sanin ‘yanci ga duk wanda ya sayar da rejistar zaben sa.
Tsohon mai baiwa shugaba Jonathan, shawara barista Ahmed Gulak, na ganin adawa har yanzu bata shirya amsar ragama daga hannun Jonathan ba. Inda yace, “ban taba zaton cewa dattijo dattijo irin Buhari zai fadi magana ya lashe, domin Buhari ya fita ya gayawa duniya gaba daya bazai sake tsayawa zabe ba, sai dai ya kawo shawara.” Ya kuma cigaba da cewa bazai yi mamaki ba idan har Buhari ya fadi wannan zabe, kasancewar mutanen da suke bin Buhari suna yaudarar sa ba zasu iya kai shi ga nasara ba.
Duk wani kamfen daga awa ashirin da hudu kafin ranar zabe ya sabawa dokar Najeriya.