Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Damuwar ‘Dan Iya Kan Yara Da Mata ‘Yan Gudun Hijira


Yara 'Yan gudun hijira a makarantar firamare a Damare, Yola3
Yara 'Yan gudun hijira a makarantar firamare a Damare, Yola3

Da yake ‘Dan Iya gwani ne wajen kira da kawo kara, shiyasa da ganin na Ikara, yace ‘dan uwa yau dai babu wata doguwar hira domin ‘dauke nake da wata damuwa ko ince larura, wadda nake ganin zaka iya bani shawara.

Na Ikara yace, to naji amma kadaina wata dawurwura ka fito fili ka gayamin matsalarka saboda na gaji da jira, ‘Dan Iya yace to na Ikara, gaskiya ina cikin damuwa saboda rayuwar yara da kuma wasu mutanen da tashe tashen hankula da masifa ke tilas tasu zuwa ‘kaura, musammam ma dai ganin yadda rayuwar kasar mu ta koma komai sai da Naira, wadda hakan nema yasa nake ganin hukumomin kasar mu sun bar yara da mata kawai a filin gudun hijira.

‘Dan Iya ya cigaba da cewa ‘dan uwa kaga kasarmu ne ake yiwa mata fyade, wasunsuma harda dukan da kambarsu a nannade, ‘yan gudun hijira kuma hukumomi sun barsu a barbade, tunaninsu kuma ana ji ana gani an barshi ya murgude, idan sun bukaci a kyautata rayuwarsu kuma sai kaji shiru an bar abin ya shude, shiyasa nake ganin lokaci yayi da hukumomin kasar mu su bi wadannan matsaloli su yade, damuwar dake dandaben dafe tunanin mata da yaran kasarmu a tunkude, saboda duk lokacin da mutum ya tsinci kanshi cikin ukuba kuma aka barshi ya dade, to zaka ga hatta tunani da basirar sa sun bi sun do’de, maimakon ma neman na kai sai kaga ya buge zuwa kofar gidan ranka ya dade.

Na Ikara yace, ‘Dan Iya gaskiya nima ina cikin damuwa, saboda yadda mata da yara a kasarmu ke cikin mummunar rayuwa, sai dai ina ganin duk da hukumomin mu sun nuna ‘dan gazawa ya zama wajibi muma ‘yan kasa mu runka bada tamu gudunwa, musani cewa fyade da tashin hankali irin na gudun hijira kan iya ‘dai ‘dai ta rayuwar bawa, saboda haka muda gwamnati musan babu wata makawa, sai mun tsaya tsayin daka wajen bada tallafin gaggawa ga mata da yaran da suka tsunci kansu cikin wata dambarwa, saboda idan Allah ya taimakemu sai kaga sun zame mana wata baiwa, wadda zata taimaka kasarmu ta rinka haskakawa.

‘Dan Iya yace, Na Ikara to sai muce Allah ya kiyaye, yasa daga yanzu mu fara ganin sauye sauye, saboda sau dayawa na kan rika hawaye idan naga an maida rayuwar yara da mata kamar ta ‘yan maye, ayi ta jifansu da muggan sunaye amma yanzu na yanke duk wani jirwaye.

XS
SM
MD
LG