Jihar Abia Na Kokarin Dakile Barkewar Zazzabin Lassa

Cutar zazzabin Lassa.

Gwamnatin jihar Abia ta ce tana iya bakin kokarinta wajen dakile barkewar cutar zazazabin Lassa a jihar, wadda ta yi sanadiyar mutuwar wata likita a wannan makon.

Kwamishinan lafiya na jihar Abia, Dr. John Ahukanna, ya ce yanzu haka mutum guda ce kadai aka sani ta kamu da cutar, kuma ana ci gaba da bincike don gano wadanda suka hadu da likitar, tare da ci gaba da fadarkar da jama’a game da cutar.

Yanzu haka dai akwai kimanin mutane 35 da ake gudanar da bincike a kansu, an kuma fadada zuwa wasu jihohi domin bincikar duk wasu marasa lafiya da marigayiyar ta taba dubawa.

A cewar Dr. Ahukanna, yanzu haka sami nasarar shawo kan cutar a jihar, hanyar rarrabawa ma’aikatu da cibiyoyin lafiya maganin cutar zazzabin Lassa.

Bayanai na nuni da cewa a yankin kudu maso gabashin Najeriya, yanzu haka an sami bullar zazzabin Lassa a jihohin Ebonyi da Imo a watan Janairun da ya gabata, inda kimanin mutane shida suka rasa rayukansu.

Domin karin bayani saurari rahotan Alphonsus Akoroigwe.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Abia Na Kokarin Dakile Barkewar Zazzabin Lassa - 2'14"