Jihohin Arewacin Nigeria, na karfafa daukan matakan hana kangarewar yara, domin tsaron kasa

Future Prowess Islamic Foundation School, Maiduguri

Gwamnatocin jihohin Arewacin Nigeria sun fi bada fifiko wajen daukan matakan horas da jami’an hana kangarewar yara.
Tun shekarun 2009; matsalar ‘yan Boko Haram ke addabar dubban jama’a a Arewacin Nigeria, a fili yake cewa‘yan Boko haram ne ke kashe dubban jama’a,ciki harda kananan yara.Bada jimawa ba Gwamnati ta bada sanarwar za’a fara horas da jami’ai na musamman da zasu fi maida hankali kan koyar da tarbiyya ga matasa a Arerwacin Nigeria, domin ko hakan zai taimaka wajen rage matsalar rashin tarbiyyar dake addabar jama’ar yankin. Ya zuwa yanzu dai anji jami’ai a cibiyar karfafa koyar da tuwasun Islama dake birnin Maiduguri suna cewa, ana matukar kokari, domin aiki ne dake bukatar nutsuwa da hakuri.

Akwai wata babbar matsalar kuma, wadda ta hada da rashin isassun kayan aiki a makarantu, musamman makarantun horas da matasa marayun da ‘yan daba suka nakasa iyayensu.Cibiyar koyar da tuwasun Islama na karbar yaran da suka zama marayu karfi da yaji saboda fadawa cikin irin wadannan rikice-rikicen, ba’a karbar ko sisin kwabo daga wajensu. Shugaban makarantar Malam Sulaiman Aliyu yace, fatansa shine makarantarsa ta sami nasarar maido da kawadayin zumunci da son zaman lafiya a zukatan daliban makarantar. Sannan yaci gaba da cewa; daga irin darussan da ake koyarwa a wannan makaranta akwai fannin kimiyya, da fannin sanin hanyar Magana da harshen Turancin Ingilishi. Akwaisu dai da dama.Ana ma koyar da harsjen larabci, da fannin ilmin kiwon lafiya. Akwai kuma fannin ilmin sanin ayyukan inji mai kwakwalwa wato ”Computer”.Akwai kuma fannonin koyon rubut da zane-zanen taswira inji Malam Sulaiman Aliyu. Ya kuma karfafa cewar ai kunga yadda wadansu daliban me ke zaune su kadai suna tunani. Da zarar an tambyesu ko me zasu iya tunawa dake damunsu, sai suk shiga kame-kame, suce wannan, kuma suce wancan.Idan har aka sami irin wannan malamai na daukan yaran a fita dasu domin halartar darasi na musamman da za’a zauna tare dasu ana tattaunawa, za’a ga suna daukan malamansu tamkar iyayensu ne, hakan kuma na kara masu kwarin gwiwa.