Jiragen Yaki: Amurka Ta Bukaci Bayani Daga Najeriya

Kotun Soji A Maiduguri Tana Shari'ar Wasu Sojoji

Fadar shugabana kasar Najeriya ta maida martani kan matsayin wadansu sanatocin Amurka biyu na kin amincewa da kudurin shugaba Trump na sayarwa Najeriya da jiragen yaki

Sanatocin da suka hada da Cory Booker na jam’iyar Democrat da Rand Paul na jam’iyar Republican sun bayyana rashin amincewarsu da kudurin shugaba Donald Trump na amincewa a saidawa Najeriya manya manyan jiragen yaki irin na zamani samfurin-A29 Super Tucano.

A cikin hirarshi da Sashen Hausa, Kakakin fadar shugaban kasar Najeriya Garba Shehu yace wannan batu ne dake tsakanin majalisar dokokin Amurka da fadar shugaban kasar, Ya bayyana cewa majalisar wakilan Amurka ta gayyaci ministan tsaron Najeriya domin yaje yayi mata bayani. Yace ministan bai sami tafiya ranar Laraba da ta gabata da ake bukata ya bayyana gaban majalisar ba sabili da wadansu matsaloli da suka bullo kai a ofishin jakadancin Amurka dake Abuja.

Sanetocin sun bayyana damuwa dangane da batun ci gaba da keta hakin bil’adama daga sojojin Najeriya, a yankin arewa maso gabashin kasar, inda suka yi misali da harin da rundunar sojin Najeriya ta kai a sansanin ‘yan gudun hijira dake Rann a Karamar hukumar Kale Balge dake jihar Borno a watannin baya.

Sai sai tun a wancan lokacin, babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sadiq Baba Abubakar, ya bayyana harin a matsayin na kuskure a wata hira da Sashen Hausa ya yi da shi a ofishinsa. Ya bayyana cewa, manufarsu ita ce su tabbata sun kare rayukan al’umma da mutuncinsu a matsayinsu na ‘yan adam ba akasin haka ba.

Tun a wancan lokacin shelkwatar rundunar ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai bincika inda aka sami kuskuren.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Hassan Maina Kaina ya hada

Your browser doesn’t support HTML5

Batun Sayar Da Jiragen yaki:2'56